Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ofishin jakadancin Sin dake Nijeriya ya kira lifyar taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar Sin
2019-09-25 11:07:28        cri

Ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Nijeriya, ya kira liyafa jiya Talata da dare, domin taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyyar jama'ar kasar Sin. Jakadan kasar Sin a Nijeriya, Zhou Pingjian, ya gabatar da jawabi yayin liyafar da ta samu halartar wakilai kimani 200, da suka hada da dukkanin jami'an diflomasiyya na ofishin, da 'yan kasar Sin dake Nijeriya da kuma wakilan kamfanonin Sin dake kasar.

Cikin jawabinsa, Zhou Pingjian ya ce, kasar Sin da kasar Nijeriya su ne manya kasashe masu tasowa, kuma muhimman abokai masu hadin gwiwa. Kana huldar dake tsakanin kasashen biyu ta zama wata alama cikin huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, har ma da dukkanin kasashen waje. A shekarar 1971 ne Sin da Nijeriya suka kulla dangantakar diflomasiyya, sa'an nan, a shekarar 2005, suka daga dangantakar dake tsakaninsu zuwa dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare, ta yadda suka karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu bisa fannoni daban daban, lamarin da ya kawo alheri ga jama'ar kasashen biyu kwarai da gaske. Kuma an yi imanin cewa, bisa kokarin da suka yi, tabbas dangantakar dake tsakanin Sin da Nijeriya za ta zama abin koyi ga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da sauran kasashen Afirka, yayin da kuma za ta karfafa dunkulewar Sin da Afirka. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China