Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CMG ya kaddamar da aikin raya kasa ta hanyar bunkasa manyan kamfanoni
2019-08-28 20:12:01        cri

Yau Laraba 28 ga wata, babban rukunin gidajen rediyo da telibijin na kasar Sin wato CMG a takaice da hukumomin da abin ya shafa da wasu shahararrun manyan kamfanoni sun kaddamar da aikin raya kasa ta hanyar bunkasa manyan kamfanoni cikin hadin gwiwa, a sa'i daya kuma, sun kaddamar da ayyukan yada manufofin jin dadin jama'a guda biyu wato "yaki da talauci ta hanyar fadakar da jama'a" da "yada manufofin jin dadin jama'a kan manyan ayyukan kasar Sin".

Gudanar da aikin raya kasa ta hanyar bunkasa manyan kamfanoni, wani mataki ne da CMG ya dauka tun bayan da ya kulla kawance da manyan kamfanoni domin raya kasa bisa manyan tsare-tsare, za a gudanar da aikin ne a dandalin CMG, ko shakka babu zai taimaka wajen fito da suna da matsayin kasa a sabon zamanin da ake ciki yanzu wadanda za su rika gudanar da cudanyar al'adu da tattalin arziki a fadin duniya a madadin kasar Sin.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China