Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CMG zai tsara shirye-shirye a jere yayin taron kolin G20 na Osaka
2019-06-27 20:29:43        cri

 

Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke halartar taron kolin kungiyar G20 karo na 14 a Osakan Japan, babban rukunin gidajen rediyo da talibijin kasar Sin wato CMG a takaice zai tsara wasu shirye-shirye a jere domin watsa su a manyan kafofin watsa labarai na kasar Japan kamar su NTV da MBS da kamfanin Yoshimoto Kogyo da Osaka-Channel da Buzz Video da sauransu.

Daga cikinsu, yau ma za a fara watsa shirin musamman game da taron na G20 mai taken "Me ka sani game da Sin da Japan" da CMG da NTV gidan telibijin mai zaman kansa mafi dogon tarihi a Japan suka tsara cikin hadin gwiwa, kuma za a sake watsa shirin a ranar 29 ga wata, a cikin shirin na tsawon awa daya, za a yi cikakken bayani kan "Kalaman Xi Jinping" cikin harshen Japananci, da sauran shahararrun shirye-shiryen da sashen Japananci na CMG ya tsara. Wannan shi ne karo na farko da ake yin bayani kan shirin "Kalaman Xi Jinping" ga al'ummun kasar Japan a babban gidan talibjin na kasar ta Japan.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China