Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manzon musamman na shugaban Sin ya halarci taron koli kan muradun ci gaba masu dorewa na MDD
2019-09-25 11:23:01        cri

Manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma mamban majalisar gudanarwar kasar, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya halarci taron koli na samun muradun ci gaba masu dorewa na MDD, jiya Talata a birnin New York, hedkwatar MDD. A jawabin da ya gabatar, Wang Yi ya ce, kamata ya yi a dora muhimmanci kan muradun kasashe masu tasowa, da hada raya tattalin arziki da muhalli da al'umma waje guda. Ya ce, dole ne a nace ga tsarin gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban da goyon bayan jagorancin da MDD ke bayarwa. Ban da wanann kuma, ya kamata a dauki matakan da suka dace don zurfafa dangantakar abota tsakanin kasa da kasa.

Wang Yi ya kara da cewa, a bana ake cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin, kuma Sin ta shiga wani sabon matakin samun bunkasuwa. Ya ce daukacin al'ummar Sinawa na kokarin samar da zaman wadata, matakin da ya kasance ka'ida mai tushe na samun bunkasuwa mai dorewa, kuma Sin ta lashi takobin kawar da talauci kafin karshen badi.

Wang Yi ya kara da cewa, Sin ta fahimci cewa, tana kan matsayin kasa mai tasowa da fuskantar karancin daidaiton samun bunkasuwa a wurare daban-daban, matakin da ya sa aka samu gibi tsakaninta da kasashe masu wadata. Har ila yau, ya ce Sin na kokarin raya shawarar "Ziri daya da hanya daya," don samun bunkasuwa tare da sauran sassan duniya, ta hanyar hadin kai da raya kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya. Ya kara da cewa, Sin na hada kai da kasashen duniya, don ba da gudunmawarsu wajen cimma muradun ci gaba masu dorewa na shekarar 2030 da samarwa Bil Adama makoma mai haske. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China