Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Sin bata amince da cin zalin sauran kasashe ba
2019-06-24 15:48:40        cri
Yau Litinin Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin ya yi shawarwari da takwararsa ta kasar Afirka ta Kudu madam Naledi Pandor a Beijing.

A yayin shawarwarin, Wang Yi yace, a matsayin muhimman wakilan kasashe masu saurin bunkasa ta fuskar tattalin arziki da kasashe masu tasowa, ya kamata Sin da Afirka ta Kudu su hada hannu da sauran kasashe wajen kiyaye babbar manufar kundin tsarin MDD da ka'idojinsa, goyon bayan ra'ayin kasancewar sassa daban daban a duniya, kiyaye muhimman ka'idojin dake shafar hulda a tsakanin kasa da kasa, kaucewa dukkan al'amurran da suka jibinci nuna bangaranci da cin zali, a kokarin kara azama kan samun zaman lafiya, ci gaba da wadata a duniya.

A nata bangaren, madam Naledi Pandor tace, kasarta da ma duk Afirka baki daya zasu hada kai da kasar Sin wajen kin amincewa da aikace-aikacen nuna bangaranci da cin zali, kiyaye ra'ayin kasancewar sassa daban daban a duniya, da kare tsarin harkokin ciniki na duniya mai bude kofa ga kowa. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China