Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya yi bayani kan sabon zagayen shawarwarin tattalin arziki da ciniki tsakanin manyan jamian Sin da Amurka
2019-08-01 10:47:45        cri

Mamban majalisar gudanarwa kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da manema labarai bayan tattaunwa da takwaransa na kasar Tailand Don Pramudwinai a jiya Laraba, inda ya yi bayani kan shawarwarin tattalin arziki da ciniki karo na 12 da ya gudana tsakanin manyan jami'an Sin da Amurka. Wang ya ce, a kwanakin baya, Sin da Amurka sun farfado da shawarwari a tsakaninsu kan tattalin arziki da ciniki, matakin da ya tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma a taron G20 na Osaka, kuma ya biya bukatun al'ummar kasashen duniya. Inda bangarorin biyu suka bayyana cikakken sahihanci a shawawarin, kuma ana fatan samun sakamako yadda ya kamata. Shawarwarin ya taka muhimmiyar rawa a matsayin mafari na sabon ci gaban da ake fatan samu. Ministan ya ce, an yi imani cewa, bangarorin biyu sun yi shawarwari cikin adalci bisa tunanin mutunta juna, da lura da batutuwan dake shafar muradun kasashen biyu, za a kai ga cimma yarjejeniyar hada kai da cin moriya tare. Matakin da ba ma kawai ya dace da muradun kasashen biyu, har ma ya dace da muradun kasa da kasa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China