Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya halarci bikin kaddamar da taron tabbatar da sakamakon da aka cimma a taron kolin FOCAC
2019-06-25 14:06:26        cri
A yau Talata, aka kaddamar da taron tabbatar da sakamakon da aka cimma a taron kolin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) a nan birnin Beijing, kuma mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar, Mr.Wang Yi ya halarci taron, inda ya karanta sakon murnar bude taron da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aiko tare da gabatar da jawabi.

Wang Yi ya yi nuni da cewa, tuni aka tsara taswirar hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka cikin sabon yanayi, amma abu mai muhimmanci shi ne yadda za a aiwatar da taswirar. Sin na son hada kai da kasashen Afirka, kuma ta dauki hakikanan matakai na cika alkawarin da ta dauka, don tabbatar da daidaito da kuma sakamakon da aka cimma a yayin taron kolin dandalin da aka gudanar a bara a birnin Beijing. Ya kara da cewa, ya kamata a tsaya ga alkiblar gina kyakkyawar makoma ta bai daya ga dukkanin al'ummomin Sin da Afirka, kuma a nace ga raya shawarar "ziri daya da hanya daya", a kuma kiyaye kasancewar bangarori daban daban da ma moriyar kasashe masu tasowa. Ya kara da cewa, babu abin da zai sauya niyyar hadin gwiwa da juna a tsakanin Sin da Afirka.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China