Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya tsokaci kan hadin kan Sin da Japan da Koriya ta kudu
2019-08-21 15:20:25        cri

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin waje na kasar Wang Yi,ya jagoranci taron ministocin harkokin waje na Sin da Japan da Koriya ta kudu karo na 9 a nan birnin Beijing a yau Laraba, kuma ya zanta da manema labarai tare da takwarorinsa na Koriya ta kudu Kang Kyung Wha da na Japan Taro Kono.

Yayin taron manema labarai, Wang Yi ya ce, mutunta tarihi da hangen nesa babban tushe ne a siyasance na hadin kan kasashen uku, mutunta juna da hadin kai da cin moriya tare, babban karfi ne dake ingiza hadin kai tsakaninsu, kuma tuntubar juna da kara amincewa da juna, fasahohi ne masu muhimmanci ga hadin kansu tare. Ya ce nacewa ga wadannan ka'idoji uku, zai sa a samu ci gaba yadda ya kamata wajen hadin kansu nan gaba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China