Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya halarci bikin murnar cika shekaru 70 da daddale yarjejeniyar Geneva
2019-09-24 10:13:51        cri
A jiya ne, memban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya halarci bikin murnar cika shekaru 70 da daddale yarjejeniyar Geneva a cibiyar MDD dake birnin New York na kasar Amurka.

Wang Yi ya bayyana cewa, bana shekaru 70 ke nan da daddale yarjejeniyar Geneva. Kasashe 196 ne suka daddale yarjejeniyar don bayyana tunaninsu na neman zaman lafiya da na kwanciyar hankali. Duk da kalubalen da ake fuskata, an yi kokarin girmama rayuwa.

Wang Yi ya bayyana cewa, Sin tana daya daga cikin kasashe na farko da suka daddale yarjejeniyar Geneva, wadda ta dauki alhakin jin kai, da samar da gudummawar jin kai ga kasashe fiye da 100. A ganin kasar Sin, ya kamata a gudanar da ayyukan jin kai bisa ka'idojin nuna daidaito ga kowane bangare, da nuna adalci, da martaba 'yancin juna, don magance maida ayyukan jin kai a matsayin na siyasa da na aikin soja. Ya kamata MDD ta kara sa kaimi da daidaita bangarori daban daban wajen gudanar da ayyukan samar da gudummawar jin kai a duniya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China