Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi nasarar harba taurarin dan Adam na Beidou guda 2
2019-09-23 11:00:51        cri

Yau da safe ne, kasar Sin ta yi nasarar harba taurarin dan Adam na Beidou guda 2, don murnar cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin.

Da misali karfe 5 da mintoci 10 na safiyar yau agogon wurin ne, kasar Sin ta yi amfani da rokar harba tauraron dan-Adam na CZ-3B wajen harba wadannan taurarin dan Adam guda 2 a cibiyar harbar tauraron bil Adama ta Xichang, wadanda suka kasance taurarin dan Adama na 47 da 48 da Sin ta harba

Bayan tafiyar sama da sa'o'i 3 da suka yi a sararin sama, taurarin dan-Adam din sun shiga falaki kamar yadda aka tsara, sun kuma fara aiki tare da samar da sakwanni na Intanet.

Tsarin zirga-zirga na tauraron dan Adam na Beidou, za su hade da sauran taurarin dan Adam a duniya don samar da hidimma mai inganci a wannan fanni. Haka kuma zai kasance tsarin samar da hidimomin manyan ababen more rayuwa na kasa da kasa ga jama'a, wanda zai ba da gudunmawa irin na kasar Sin wajen raya kyakkyawar makomar bil Adam baki daya a duniya.

Wannan shi ne karo na 312 da aka yi amfani da rokar dakon taurarin dan-Adam wajen harba taurarin dan Adam samfurin CZ. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China