Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta kulla dangantakar diplomasiyya da kasar tsibiran Solomon
2019-09-21 20:00:14        cri
A yau Asabar ne, memban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya yi shawarwari da takwaransa na kasar tsibiran Solomon Jeremiah Manele a nan birnin Beijing, tare da daddale hadaddiyar sanarwar kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Sanarwar ta bayyana cewa, gwamnatin kasashen biyu sun amince da raya dangantakar dake tsakaninsu bisa tushen girmama ikon mallaka da cikakken yankunansu, da kaucewa tsoma baki kan harkokin cikin gida, da tabbatar da adalci, da samun moriyar juna, da kuma zama tare cikin lumana. Gwamnatin kasar tsibiran Solomon ta amince da kasar Sin daya tak a duniya, kana gwamnatin kasar Sin ita ce halatacciyar gwamnatin kasar, kuma yankin Taiwan yanki ne na kasar Sin. Gwamnatin tsibiran Solomon ta yanke huldar dake tsakaninta da yankin Taiwan, tare da yin alkawarin ba za ta sake kulla huldar dake tsakaninta da Taiwan ba. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China