Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan kasar Sin dake Najeriya ya kai ziyara Imo da Bayelsa
2019-09-19 09:35:56        cri

Jakadan kasar Sin dake kasar Najeriya mista Zhou Pingjian ya kai ziyara jihohin Imo da Bayelsa tsakanin ranakun 17 zuwa 18 ga watan Satumba.

A yayin da yake tattaunawa da bangaren Najeriya, Zhou ya bayyana cewa, kasarsa na son kara yin cudanya da kananan hukumomin kasar, da karfafa hadin kai a fannonin zuba jarin samar da kayayyaki da dai sauransu, kana da tabbatar da nasarorin da aka cimma a yayin taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Afirka tare, da kokarin raya shawarar "Ziri daya da hanya daya" cikin inganci, da kuma kara cikar da abubuwan dake shafar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da Najeriya, don raya al'umma mai kyakkyawar makomar kasashen biyu.

Bangaren Najeriya ya bayyana cewa, gaggaruman nasarorin da kasar Sin ta cimma wajen raya kanta ya karfafa imanin kasashen Afirka, ciki har da Najeriya da kuma kasashe masu tasowa wajen farfado da kansu. Yanzu haka, gwamnatoci a mataki daban-daban a Najeriya suna kokarin inganta muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a, da kokarin raya tattalin arziki ta hanyoyi daban daban a dukkan fannoni, da gaggauta yunkurin raya masana'antu. Haka kuma suna fatan kara yin mu'amala da hadin kai tare da kasar Sin a fannoni daban daban, da nufin cimma nasara tare. Ban da wannan kuma, kasar Najeriya ta himmatu wajen kyautata yanayin gudanar da harkokin cinikayya, da kara bullo da manufofin nuna gatanci, don kara jawo kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a kasar. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China