2019-09-20 09:25:59 cri |
Hukumar raya kasa da yin gyare-gyare ta kasar Sin (NDRC) ta wallafa a shafinta na Intanet cewa, gwamnatin kasar ta lashi takwabin taimakawa ayyukan kawar da talauci ta hanyar amfani da Intanet, a wani mataki na samun nasara a yaki da talauci da mahukuntan kasar ke yi.
Wani tsari da hukumar ta fitar sun nuna cewa, matakin zai kara fadada amfani da Intanet a yankunan kasar dake fama da matsalar talauci.
Don haka, tsarin ke kira da a kara amfani da Intanet, da muhimman bayanai, da wasu shafukan Intanet da kwaikwayon tunanin dan-Adam a fannin aikin gona da yankunan karkara.
Haka kuma, gwamnatin za ta goyi bayan harkokin cinikayya ta yanar gizo a yankunan karkara, a matsayin wani bangare na matakan kawar da talauci, da fadada hanyar ta yadda yankunan dake fama da talauci, za su rika sayar da amfanin gonansu cikin sauki.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China