Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar wakilan kasar Sin sun kara tashi zuwa Amurka
2019-09-18 14:05:23        cri
Tawagar wakilan kasar Sin karkashin jagorancin mataimakin shugaban ofishin kula da harkokin kudi na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kana mataimakin ministan kudin kasar, Liao Min, ta tashi zuwa Amurka, bisa gayyatar Amurka, don share fagen shawarwarin tattalin arziki da ciniki da za a gudanar tsakanin manyan jami'an kasashen biyu karo na 13 a wata mai zuwa a birnin Washington.

Tun bayan da kasashen biyu suka tsai da kudurin gudanar da shawarwarin, sassan biyu na tuntubar juna yadda ya kamata. Kasar Sin a nata bangaren ta dauki matakai na cire karin harajin da ta sanya kan wasu nau'o'in kayayyaki 16 da take shigowa daga Amurka. Daga nasa bangaren kuma, shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya sanar da jinkirta sanya karin haraji kan kayayyakin da kasarsa ke shigowa daga kasar Sin.

Ana fatan Amurka za ta yi amfani da wannan damar da ake da ita ta daidaita matsalar ciniki, kuma ta hada kai da kasar Sin, don samar da yanayi mai kyau na yin shawarwari, wanda hakan zai amfana wa kasashen biyu da ma duniya baki daya.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China