Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin kasar Sin ya yi bayani a kan harkokin nukiliya na kasar
2019-09-18 10:07:02        cri
A ranar 16 ga wata, an gudanar da taron hukumar makamashin nukiliya ta duniya karo na 63 a birnin Vienna.

A jawabin da ya gabatar a yayin babbar muhawarar da aka gudanar, mataimakin shugaban hukumar makamashin kasar Sin Zhang Jianhua ya jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin na dora matukar muhimmanci a kan tsaron nukiliya. A yayin da ake tabbatar da saurin bunkasuwar makamashin nukiliya mai dorewa a kasar, an kuma kiyaye tsaron nukiliyar. A watan Satumban shekarar 2019, a karo na farko kasar Sin ta gabatar da takardar bayani game tsaron nukiliyar kasar, inda aka yi cikakken bayani a kan ka'idoji da manufofin kasar ta fannin tabbatar da tsaron nukiliya.

Zhang ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan hukumar makamashin nukiliya ta duniya, ta yadda za ta kara ba da gudummawarta ta fannonin bunkasa fasahohin nukiliya da samun dauwamammen ci gaba da inganta tsaron nukiliya da hana yaduwar makaman nukiliya da ma daidaita matsalolin da ke janyo hankulan duniya ta hanyar yin shawarwari.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China