Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta inganta takararta a fannin sufuri na duniya
2019-09-20 10:23:52        cri
Kasar Sin na da niyyar kara takararata a bangaren sufuri na duniya, ta hanyar kara fadada hanyoyin sufuri da kara saurin lokacin tafiye-tafiye.

A cewar wani daftari da majalisar gudanarwar kasar da kwamitin tsakiya na JKS suka fitar, ya zuwa shekarar 2035, Kasar za ta kafa wani cikakken tsarin sufuri na zamani.

Kasar Sin za ta samar da wani tsarin sufuri a cikin gida, wanda zai rage lokacin zirga zirga a cikin birane zuwa sa'a 1, yayin da tsawon tafiya zuwa birane makwabta zai tsaya kan sa'o'i 2, sai kuma zuwa sauran manyan birane na fadin kasar da zai tsaya kan sa'o'i 3.

Kammala aikin inganta sufurin, zai saukaka jigilar kayayyaki ko sakonni a cikin birane zuwa rana 1, yayin da tura kayayyaki zuwa kasashe makwabta zai dauki yini 2, inda zuwa sauran biranen dake fadin duniya kuma zai dauki kwanaki 3.

Kasar za kuma ta inganta amfani da fasaha a fannin sufuri, ta hanyar amfani da manyan bayanai da kwaikwayon tunanin dan Adam, da kuma rungumar tsarin raya muhalli ta hanyar tsimin makamashi da takaita gurbatar yanayi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China