Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararrun kasashen waje: an tabbatar da zaman al'umma mai jituwa a jihar Xinjiang ta Sin
2019-08-03 16:20:18        cri
Kwanan baya, kwararru da masana da suka fito daga kasashen Faransa, Italiya, Poland, New Zealand, Rasha, Pakistan, Thailand da sauransu sun ziyarci jihar Xinjiang ta kasar Sin.

Bayan ziyarar, Francesca Manenti ta cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta kasar Italiya, ta bayyana cewa, "na gano jihar Xinjiang na kara samun cigaba, kuma an kafa zaman al'ummar dake kunshe da kowa da kowa a jihar. Ayyukan ta'addanci da aka tayar a yankin a baya, halinsu kamar wanda aka samu ne a Turai a 'yan shekarun da suka gabata. Ra'ayin ta'addanci na kawo illa ga duk duniya, don haka, ya kamata kasashe daban daban su hada kai don tinkarar ta'addanci tare, da kuma kafa wata al'umma mafi samun kwanciyar hankali da yin hakuri da juna."

A nasa bangaren, mai jan akalar shiri na gidan talibijin na kasar Paskistan Sultan Mahmoud Harry ya ce, "a masallatai, na gano yadda gwamantin kasar Sin ke girmama 'yancin jama'a wajen bin addininsu, kuma na fahimci hakikanin halin da musulman jihar ke ciki a watan azumi. A ganina, a yayin da gwamnatin kasar Sin ke kokarin yaki da ta'addanci bisa doka, a sa'i daya kuma tana mai da hankali wajen kawar da tsattsauran ra'ayi ta hanyar neman ci gaba." (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China