Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xinjiang za ta samarwa matasa 10,000 guraben ayyukan yi
2019-08-01 10:40:25        cri
Jihar Xinjiang Uygur mai cin gashin kai dake shiyyar arewa maso yammacin kasar Sin za ta samarwa matasan yankin 10,000 damammakin samun horon sanin makamar aiki cikin shekaru 3 masu zuwa da nufin bunkasa samar da guraben ayyukan yi, hukumomin gudanarwar yankin ne suka tabbatar da hakan.

Sashen kula da ma'aikata da walwalar jama'a na yankin Xinjiang ya sanar cewa za'a samar da damammakin kimanin 4,000 a wannan shekarar, sannan a samar da 3,000 a shekarar 2020, kana a samarwa mutane 3,000 damammaki a shekarar 2021.

Wadanda za su ci gajiyar shirin sun hada da mutanen da suka kammala karatun jami'a da kwalejoji sun shafe shekaru biyu amma ba su samu ayyukan yi ba, da matasan da ba su da aikin yi 'yan shekaru tsakanin 16 zuwa 24 da haihuwa. Daga cikinsu, za'a fi bada fifiko ga wadanda ke fama da kangin talauci, da masu karancin samun kudaden shiga, da iyalan da ba su da takamammiyar sana'a, sai kuma mutanen da ba su da wata kwarewar aiki.

Shirin ba da horon zai fara ne daga watanni 3 zuwa 12. Wadanda za su samar da guraben aikin yi za su bada rangwame ga tsarin inshorar masu halartar shirin bada horon.

Jihar Xinjiang Uygur mai cin gashin kai ta samar da sabbin guraben ayyukan yi 353,400 ga mazauna yankin a watanni shidan farko na shekarar 2019. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China