Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta fitar da takardar bayani kan koyar da ilimin sanaoi a Xinjiang
2019-08-16 13:49:50        cri

Takardar bayani da ofishin yada labarai da wayar da kan jama'a na majalisar gudanarwar kasar Sin ya wallafa a yau Jumma'a, ta ce ta'addanci da tsattsauran ra'ayi su ne makiya iri guda na dukkan bil adama, kuma yaki da su hakki ne da ya rataya akan dukkan al'ummomin duniya.

A cewar takardar bayanin, yaki da ta'addanci hakki ne da ya rataya akan duk gwamnatin da ta san ya kamata, da aiki bisa tanadin dokoki domin kawar da ta'addanci da ya yi kanta a zukatan al'umma da tsattsauran ra'ayi dake barazana ga rayuwa da tsaron jama'a, da nufin kare kima da darajarsu da hakkinsu na rayuwa da lafiya da samun ci gaba da kuma more muhalli mai cike da zaman lafiya da zamantakewa cikin kwanciyar hankali.

Ta kara da cewa, domin magance alamomi da tushen abubuwan dake haifar da matsalolin biyu, da daukar matakan kariya da na mayar da martani, jihar Xinjiang ta kafa cibiyoyin koyar da sana'o'i bisa tanadin doka, domin kare yaduwar ta'addanci da kaifin kishin addini, da magance aukuwar ayyukan ta'addanci da kare hakkokin rayuwa da na lafiya da ci gaban jama'ar kabilu daban-daban, tana mai cewa, tuni aka cimma kyawawan sakamako. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China