Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Antonio Guterres na fatan shugabanni mahalarta babban zauren MDD su cika alkawuransu
2019-09-19 14:10:51        cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana a jiya Laraba a hedkwatar MDD dake birnin New York cewa, yanzu ana cikin wani muhimmin lokaci na samun bunkasuwa a fannoni daban-daban a duniya, ya kamata kasashen duniya su gaggauta kara hada kai, don fito da hanyar da ta dace ta warware matsalolin dake jawo hankalin kasa da kasa. Haka kuma yana fatan shugabannin mahalarta babban zauren MDD za su cika alkawuran da suka yi a yayin taron.

A mako mai zuwa ne, ake sa ran shugabanni da manyan wakilan kasa da kasa za su halarci babbar muhawara da taron koli na babban zauren MDD na wannan karo. Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, zai jagoranci tawagar kasar Sin a taron, kuma a matsayinsa na wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, Wang Yi zai halarci taron koli na yaki da matsalar sauyin yanayin duniya da taron koli muradun ci gaba mai dorewa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China