Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Afirka mambobin kwamitin tsaron MDD sun yi kira da a dage wa Sudan takunkumi
2019-09-11 09:25:10        cri

Kasashen nahiyar Afirka 3 mambobin kwamitin tsaron MDD, da kuma kungiyar tarayyar Afirka ta AU, sun yi kira da a dage wa kasar Sudan dukkanin takunkumai na kasa da kasa, bayan kafa gwamnatin rikon kwarya da fararen hula ke jagoranta a kasar.

Wata sanarwar da jakadan kasar Cote d'Ivoire a MDD Leon Kacou Adom ya karanta, ta ce Cote d'Ivoire, da Equatorial Guinea da Afirka ta Kudu, da ma kungiyar AU baki daya, sun bukaci daukacin sassan masu ruwa da tsaki da su dagewa Sudan takunkumai da ke wuyan ta, ciki hadda cire ta daga jerin kasashe dake tallafawa ta'addanci.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, ofishin ayyukan wanzar da zaman lafiya da tsaro na kungiyar AU, ya amince ya dage takunkumin watanni 3 da kungiyar ta sanyawa Sudan, biyowa bayan kyakkyawan sauyin da aka samu a kasar.

Sanarwar ta kuma yi fatan sabuwar gwamnatin Sudan, za ta aiwatar da manufofin da aka tsara karkashin yarjejeniyar sulhu, ta kuma tabbatar da gudanar da zabukan 'yan majalisa da na shugaban kasa, matakin da zai kai ga mika mulki ga halastacciyar gwamnati, da wanzuwar zaman lafiya da daidaito mai dorewa. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China