Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na son inganta hadin gwiwa da tattaunawa yayin taron hukumar kare hakkin bil adama ta MDD
2019-09-07 16:18:14        cri
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Chen Xu, ya ce kasarsa na fatan dukkan bangarori masu ruwa da tsaki, za su goyi bayan tattaunawa da hadin gwiwa, yayin taron hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD dake karatowa.

Chen Xu ya bayyana haka ne, yayin wani taron manema labarai a hedkwatar MDD dake Geneva, gabanin taro karo na 42 na hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD da za a yi daga 9 zuwa 27 ga watan Satumba.

Ya ce ya kamata komai ya kasance bisa cimma matsaya daya maimakon yin fito na fito. Yana mai cewa, Sin ba za ta taba amincewa da dabi'ar nuna yatsa ko amfani da wani kudurin na wata kasa domin matsa mata lamba ba.

Ya ce suna fatan hukumar a wannan karon, za ta mayar da hankali kan tabbatar da aiwatar da ajandar ci gaba da ake son cimmawa ya zuwa shekarar 2030, da yaki da wariyar launin fata da ta'addanci.

Wakilin na kasar Sin, ya ce kasashe na bukatar daidaita kare duk wani nau'in hakkin dan Adam da kara zuba jari kan bangaren tattalin arziki da tabbatar da hakkokin zaman takewa da na al'adu da na samun ci gaba, domin ci gaba ya kunshi komai da komai. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China