Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakataren MDD ya yi Allah wadai da hare-haren da aka kai kan na'urorin hakar man Saudiya
2019-09-16 09:13:39        cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da hare-haren da aka kai ranar Lahadi kan kayayyakin hakar man kamfanin Aramco dake gabashin kasar Saudiya.

Mr Guterres ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da kakakinsa Stephane Dujarric ya rabawa manema labarai. Wasu alkaluma da ba a tabbatar ba, sun bayyana cewa, fashewar da ta faru, ta shafi yawan danyen man da ake hakowa da a kalla ganga miliyan 5.7 ko kwantankwacin kaso 50 cikin 100 na man da kamfanin yake hakowa.

Da yake karin haske kan lamarin, ministan makamashi na kasar Saudiya Abdulaziz bin Salman Al Saud ya sanar a jiya Lahadi cewa, hare-haren jirage marasa matukan, sun kai ga dakatar da aikin hako mai a kamfanin da aka nufa na dan wani lokaci.

Gidan talabijin na al- Masirah mallakar mayaka Houthi na kasar Yemen, ya ruwaito mayakan suna sanar da daukar alhakin kai hare-hare da jirage marasa matuka guda biyu kan nau'rorin kamfanin man Aramco dake gabashin kasar Saudiya a ranar Asabar da ta gabata.

Da asubahin ranar Asabar ne, aka ba da rahoton kai hare-hare da jirage marasa matukan inda aka ji karar fashewa da dama a kamfanin hakar man Aramco dake Khurais da Abqaiq dake gabashin Saudiya, lamarin da ya haddasa gobara, ko da yake an shawo kanta daga bisani. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China