Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin a MDD ya yi kira da a goyi bayan zaben shugaban kasa a Guinea-Bissau
2019-09-11 10:07:43        cri
Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya yi kira ga 'yan kasar Guinea-Bissau da sauran sassan kasa da kasa, da su mara baya ga shirin da ake yi na gudanar da zaben shugaban kasa a Guinea-Bissau.

Wakilin na Sin ya yi kiran ne, yayin da yake tsokaci gaban mambobin kwamitin tsaron MDD. Ya ce kasarsa na fatan dukkanin masu ruwa da tsaki za su goyi bayan nasarar zaben dake tafe a watan Nuwamba mai zuwa. Ya ce akwai bukatar kasashen duniya su kara kaimi, wajen ci gaba da samar da tallafin kwarewa, da kudade, da tsare-tsaren gudanar da zaben, bisa bukatun gwamnatin Guinea-Bissau.

Wu Haitao, ya ce kamata ya yi daukacin sassan Guinea-Bissau su yi aiki yadda ya kamata, domin kare bukatun al'ummar kasar cikin dogon lokaci, matakin da zai taimaka wajen gina yarda da juna, da samar da damar tattaunawa da aiwatar da shawarwari, da cimma matsaya guda, da magance sabani, da karfafa damar samun ci gaba a sashen siyasa, da yin shiri mai ma'ana gabanin zaben shugaban kasa. Kaza lika ya kamata sassan su maida hankali ga inganta yanayin rayuwar jama'a, da ingiza samar da daidaito da ci gaba a sassan kasar baki daya. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China