Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude babban zauren MDD karo na 74
2019-09-18 10:32:55        cri

An bude babban zauren MDD karo na 74 a jiya Talata a hedkwatar MDD dake birnin New York.

A jawabinsa na hude taron, babban sakataren majalisar António Guterres ya bayyana cewa, shekarar 2020 na da muhimmanci sosai wajen cimma burin samun bunkasuwa mai dorewa, da daukar matakan tinkarar sauyin yanayi, ya kamata mu karfafawa jama'a gwiwa cewa, ayyukan da MDD ke gudanarwa na da alaka sosai da su, kuma a cewarsa, gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban, ita ce hanyar da ta dace wajen tinkarar kalubalolin da duniya ke fuskanta yauzu.

A nasa jawabin sabon shugaban babban zauren na wannan karo Tijjani Muhammad Bande ya bayyana cewa, taron na wannan karo nan zai mai da hankali kan cimma muradun samun bunkasuwa mai dorewa, wato kawar da talauci da yunwa da ba da ilmi mai inganci, da kuma daukar matakin tinkarar sauyin yanayi da kara fahimtar juna tsakanin kasa da kasa da sauransu. Babban zauren zai kuma ci gaba da tabbatar da tsaro da zaman lafiya a duniya, kuma zai kara hadin kai da cudanya da kwamitin sulhu da sakatariyar MDD don kandagarkin rigingimu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China