Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Geneva: an shirya taron yaki da tsattauran raayi da kiyaye hakkin dan Adam a Xinjiang
2019-09-17 10:27:35        cri

Yayin da kwamitin kula da harkokin kiyaye hakkin dan Adam na MDD yake gudanar da taronsa karo na 42, ta kuwa hukumar kare hakkin dan Adam ta kasar Sin ta shirya taro ne, kan yadda kasar Sin take kiyaye hakkin dan Adam da yaki da tsattsauran ra'ayi a jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta a birnin Geneva a ranar 16 ga wata. Wasu kwararru sun yi bayani kan matakan da ake dauka na yaki da tsattsauran ra'ayi a Xinjiang, kyawawan fasahohi da jihar ta samu da yadda ake kiyaye hakkin dan Adam a jihar. Wakilai fiye da 50 daga wasu kasashe, kungiyoyin kasa da kasa da hukumomi masu zaman kansu sun halarci taron.

Chang Jian, darektan cibiyar nazarin hakkin dan Adam da ke jami'ar Nankai ta kasar Sin ya yi bayani da cewa, matakan da mahukuntan jihar Xinjiang suke dauka a jere, sun taimaka wajen hana yaduwar tsattsauran ra'ayi da yunkurin nuna karfin tuwo. Tun bayan watan Disamban shekarar 2016 har zuwa yanzu, watanni 33 ke nan da ba a samu abkuwar hare-haren ta'addanci a jihar ta Xinjiang ba. Kana a shekarar 2018 da ta gabata ne mutane sun yi tafiye-tafiye fiye sau miliyan 150 a Xinjiang, adadin da ya karu da kaso 40 ko fiye da haka bisa makamancin lokaci na shekarar bara. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China