Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashe da dama sun nuna goyon baya ga matsayin Sin game da batun Xinjiang da Hong Kong
2019-09-12 11:05:11        cri
A gun taron majalisar hakkin dan Adam ta MDD karo na 42 da aka gudanar tun daga ranar 10 zuwa 11 ga wannan wata, wakila daga kasashe da kungiyoyin da ba na gwamnati ba da dama sun nuna yabo ga kasar Sin bisa kokarinta na yaki da ta'addanci da kawar da tsattsauran ra'ayi a yankin Xinjiang, kuma sun yi kira ga masu zanga-zanga na yankin Hong Kong na kasar Sin da su dakatar da tada rikici, da kuma nuna kin amincewa da matakin wasu kasashen duniya na tsoma baki cikin harkokin yankin Hong Kong.

Zaunannen wakilin kasar Yemen dake birnin Geneva ya taba kai ziyara cibiyar horar da kwararru ta Xinjiang, inda ya ce kasarsa ta yabawa kasar Sin domin ta yi kokari wajen bada ilmi, da samun ci gaba, da kawar da talauci, da yaki da ta'addanci da sauransu, musamman nasarorin da aka samu a yankin Xinjiang.

Wakilai da dama na kungiyoyi da ba na gwamnati ba sun yi tir da rikicin da aka tada a yankin Hong Kong. Kungiyar hadin gwiwar mata ta yankin Hong Kong ta yi Allah wadai da rikicin da masu tsattsauran ra'ayi na yankin suka tada, a ganinta tsattsauran ra'ayi da rikici za su kawo babbar illa ga yankin. Kungiyar kula da harkokin MDD ta kasar Sin ta bayyana cewa, zanga-zangar da ake yi a yankin Hong Kong ta yi illa ga zaman lafiya, ta gurguta zaman rayuwar jama'a, kuma ta yi kira ga kasa da kasa da su nuna goyon baya ga gwamnatin yankin Hong Kong a kokarin mayar da dokoki da odar zamantakewar al'umma. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China