![]() |
|
2019-07-25 13:45:50 cri |
Takardar bayanin dai an fitar da ita ne a Alhamis din nan, tana kuma da jigon "Daidaito, tafiya tare, da kuma raba daidai: shekaru 70 na kare hakkokin masu bukata ta musamman a janhuriyar al'ummar kasar Sin."
Yanzu haka dai Sin na da al'umma masu bukata ta musamman da yawan su ya kai miliyan 85. Kuma takardar bayanin ta nuna cewa, cikin shekaru sama da 70 tun bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin a shekarar 1949, jami'iyyar JKS da gwamnatin Sin, na sanya bukatun al'ummar kasar sama da komai, ta hanyar ba da kulawa ga rukunin al'ummu masu fama da wahalhalu, tare da shigar da su, da damawa da su, da samar musu damar cin gajiya daga sassan ci gaban tattalin arzikin kasar.
Takardar ta kuma ce, za a ci gaba da aiwatar da matakan inganta tsare tsare na kare bukatun wadannan rukuni na al'umma, ba tare da nuna wariya ba, da tabbatar da kyautatuwar rayuwar su, da inganta yanayin da suke ciki, tare da tabbatar da cewa, sun samu zarafin shiga a dama da su a harkokin da suka shafi ci gaban kasa, da raba moriyar hakan daidai wa daida. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China