Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a bude cibiyar watsa labaran bikin cika shekaru 70 da kafa sabuwar kasar Sin a 23 ga Satumba
2019-08-30 19:46:18        cri

Rahotanni daga kasar Sin na cewa, a ranar 23 ga watan Satumba ne, za a bude cibiyar watsa labaran bikin cika shekaru 70 da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, da za a gudanar a ranar 1 ga watan Oktoba a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

An dai kafa cibiyar bikin ne a otel din Beijing Media Center, inda za a rika yin hirarraki da jami'an da abin ya shafa, da shirya tarukan 'yan jaridu, da samar da muhimman bayanai da suka shafi bikin, da samar da hidimomin ga manema labarai.

Haka kuma, za a samar da shafi da dandalin WeChat a cibiyar, da manema labarai za su rika amfani da su a hukumance.

Manema labarai daga yankunan musamman na Hong Kong da Macao da Taiwan na kasar Sin, da 'yan jaridu na ketare, za su iya yin rijista ta yanar gizo ta wannan adireshi http;//reg70prc.zgjx.cn, tun daga ranar 22 ga watan Agusta zuwa 8 ga watan Satumba. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China