Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a gudanar da kasaitaccen bikin murnar cika shekaru 70 da kafa jamhuriyar jamaar Sin a ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa
2019-08-29 11:42:02        cri

A ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa, za a gudanar da kasaitaccen bikin murnar cika shekaru 70 da kafa jamhuriyar jama'ar Sin a filin Tian'anmen dake birnin Beijing, hedkwatar kasar. A gun bikin, babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar, kana shugaban kasar, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin koli na soja na kasar, Mr. Xi Jinping zai gabatar da muhimmin jawabi. Bayan bikin, za a gudanar da faretin soja da ma babban macin al'umma.

Sannan, za a bada lambobin yabo da na girmamawa a matsayin kasa ga fitattun mutanen da al'ummar kasar suka amince da gudummarwarsu ta fannonin raya ci gaban kasar mai tsarin gurguzu da ma tsaron kasar, da kuma 'yan kasashen waje da suka bada babbar gudummawa ta fannin raya kasar Sin da ingiza hadin gwiwar kasar Sin da kasashen ketare da ma kiyaye zaman lafiyar duniya, har wa yau da fitattun mutanen da suka bada babbar gudummawa a sana'o'insu daban daban, wadanda kuma suke da kwarjini a tsakanin al'umma. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ne zai mika musu lambobin yabo shi da kansa.

A ranar da dare kuma, za a gudanar da shagulgulan murnar ranar a filin na Tian'anmen, inda shugabannin kasar za su halarci shagulgulan tare da wakilan al'umma, za su kuma kalli wasannin nuna fasaha da kuma wasan wuta da za a nuna.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China