Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mayar da kamfanonin Afirka ta Kudu mallakin Najeriya ba zai haifar da da mai ido ba in ji wani masani
2019-09-10 10:36:01        cri

Shugaban tsangayar koyar da ilimin tattalin arziki da kimiyyar kasuwanci a jami'ar Witwatersrand dake Afirka ta Kudu Jannie Rossouw, ya ce shawarar da wasu ke bayarwa game da mayar da wasu kamfanonin Afirka ta Kudu mallakin gwamnatin Najeriya ba za ta haifarwa kasar da mai ido ba.

Malamin ya ce, daukar wannan mataki zai gurgunta tsarin kasuwanci a nahiyar Afirka, zai kuma karya gwiwar masu sha'awar zuba jari dake sassan nahiyar.

Kalaman Mr. Rossouw na zuwa ne, bayan da shugaban jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya Adams Oshiomhole, ya yi kira ga mahukuntan kasar da su duba yiwuwar mayar da kamfanonin Afirka ta Kudu mallakin Najeriya, biyowa bayan hare-haren kin jinin baki da suka auku a Afirka ta Kudun.

Oshiomhole ya yi wannan tsokaci ne a Jumma'ar da ta gabata, yana mai cewa, akwai bukatar Najeriya ta duba yiwuwar karbe ragowar jarin da kamfanin sadarwa na MTN na Afirka ta Kudu ke da shi, da ma sauran wasu kamfanonin kasar dake hada-hada a Najeriya.

Rahotanni dai sun ce tun daga karshen watan da ya gabata, an rika samun hare-haren nuna kin jinin baki mazauna Afirka ta Kudu, ciki hadda wasu 'yan Najeriya da lamarin ya rutsa da su. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China