Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD:Ma'aikatan agaji 37 ne suka mutu a shekaru 10 na hare-haren Boko Haram a Najeriya
2019-08-20 19:26:01        cri
Ofishin kula da harkokin jin kai na MDD (UNOCHA), ya tabbatar da cewa, ma'aikatan jin kai 37 ne suka gamu da ajalinsu, cikin shekaru goma da mayakan Boko Haram suka shafe suna kaddamar da hare-hare a Najeriya. Yana mai kira da a kare rayukan mutane dake gudanar da ayyukan jin kai a kasar.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar a Abuja, babban birnin Najeriya, wanda kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafenta, ta bayyana cewa, tun shekarar 2018, hare-haren da ake kaiwa ma'aikatan jin kai a yankin arewa maso gabashin Najeriya, tungar mayakan na Boko Haram sun kara tsanani.

Hari na baya-bayan da shi ne na ranar 18 ga watan Yuli, lokacin da mayakan na Boko Haram suka kaiwa jerin gwanon motocin dake kai ma'aikatan jin kai yankin Damasak na jihar Borno, daya daga cikin jihohi uku dake yankin arewa maso gabashin kasar da hare-haren mayakan suka fi muni.

A wancan harin, an halaka direba guda da wasu ma'aikata 6, ciki har da ma'aikatan lafiya 4 da direbobi 2 da aka yi garkuwa da su.

Ma'aikatan dai na kan hanyarsu ta samar da taimakon ceton ran wasu mutane da iyalai da matsalar jin kai dake faruwa a yankin arewa maso gabashin Najeriya ta shafa, lokacin da mayakan na Boko Haram suka yi musu kwanton bauna.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China