Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO tana duba yiwuwar ayyana Najeriya kasar da tayi ban kwana da cutar Polio
2019-07-24 10:22:18        cri
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) tace tana nazarin wasu alkaluma da ta tattara daga Najeriya game da ikirarin da kasar ta yi na rashin samun rahoton bullar cutar polio a fadin kasar a shekaru ukun da suka gabata, wata jami'ar hukumar ta WHO ce ta bayyana hakan a jiya Talata.

Charity Warigon, kakakin hukumar WHO dake Najeriya, ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, ofishin hukumar lafiyar ta duniya dake Najeriya ya bayyana farin cikinsa bisa ga kwazon da Najeriyar ta nuna a kokarin kawar da cutar polio daga fadin kasar, kana hukumar tana la'akari da irin kokarin da gwamnatin Najeriyar ke yi wajen kawar da cutar baki daya daga kasar.

Warigon ta ce, rahoton karshe da aka samu na bullar cutar polio a Najeriya shi ne na ranar 21 ga watan Augastan shekarar 2016.

Jami'ar ofishin hukumar WHO ta Najeriya ta nanata kokarin Najeriyar wajen cimma manyan nasarori, musamman wajen gina tunanin al'umma na amincewa da karbar alluran rigakafin cutar da jajurcewar da suka nuna game da shirin yaki da cutar.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China