Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojojin Najeriya zata tura karin jiragen yaki zuwa yankuna masu matsalar tsaro
2019-08-25 16:13:13        cri
Babban hafsan sojojin saman Najeriya yace, hukumar sojojin kasar zata tura karin jiragen saman yaki zuwa yankunan kasar da ake fama da matsalolin rashin tsaro, domin tallafawa dakarun sojojin kasa bisa irin namijin kokarin da suke yi.

Sakamakon hakan, a halin yanzu rundunar sojojin saman Najeriyar ta fara gyara wasu daga cikin kananan jiragen yakin da aka jibge su tsawon lokaci ba'a amfani dasu a wasu sansanonin sojin kasar, Sadique Abubakar, babban hafsan sojojin saman Najeriya ya bayyana hakan ga manema labaru a birnin Fatakol dake kudancin kasar.

A cewar Abubakar, a halin da ake ciki mayakan kungiyar 'yan ta'adda na Boko Haram sun yi mummunar barna a shiyyar arewa maso gabashin kasar cikin shekaru sama da goma da suka shude, sannan ga karin barazanar tsaro ta mayakan 'yan bindiga da suka addabi shiyyar arewa maso yammacin kasar, suna cigaba da kaddamar da munanan hare hare, da yin garkuwa da mutane.

Yace jiragen saman yakin za'a turasu ne wadandan shiyyoyi guda biyu, domin fatattakar masu aikata muggan laifuka.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China