Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Nijeriya zai ziyarci Afrika ta kudu biyo bayan hare-haren kin jinin baki
2019-09-08 16:26:16        cri
Fadar Shugaban kasar Afrika ta kudu, ta sanar da cewa, Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, zai ziyarci kasar a wata mai zuwa, biyo bayan jerin hare-haren kin jinin baki da suka wakana a kasashen biyu.

Muhammadu Buhari zai tattauna da takwaransa na Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa, domin karfafa dangantakar kasashen biyu da kuma hada hannu wajen samar da hanyoyin tunkarar kalubalen da jama'a da kasuwancinsu ke fuskanta a kasashen biyu.

An shafe kwanaki ana gudanar da zanga-zanga a Afrika ta Kudu, inda ake kai hari kan shagunan baki, ciki har da na 'yan Nijeriya. An kashe akalla mutane 10, 2 daga cikinsu 'yan kasashen waje, a rikicin da ya fara a Pretoria babban birnin mulkin kasar, wanda kuma ya bazu zuwa birnin Johannesburg.

A sa'i daya kuma, babban kamfanin sanadarwa na Afrika ta Kudu wato MTN, da babban kantin sayar da kayayyaki na Shoprite, sun rufe dukkan shagunansu da cibiyoyin hada-hadarsu a Nijeriya, biyo bayan harin da aka kai harabobinsu.

Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya tattauna a ranar Juma'a da manzon musammam na shugaban Nijeriya, Ahmed Rufai Abubakar, dangane da rikicin dake gudana a kasashen 2.

Ahmed Abubakar, ya bayyana damuwar Shugaba Buhari game da hare-haren da ke aukuwa a Afrika ta Kudu tare da bayyana kudurinsa na girmama burin bai daya na kasashen biyu na samar da ci gaba a nahiyar Afrika.

Har ila yau, fadar Shugaban kasar ta ce, Shugaba Buhari ya kuma yi alkawarin gwamnatin Nijeriya za ta dauki mataki kan take dokoki da kai hari kan dukiyar Afrika ta Kudu.

Shi kuwa shugaba Ramaphosa, jaddada dangantakar kasashen biyu ya yi a matsayin mai karfi da karko, yana mai cewa, za su ci gaba da tsayawa tsayin daka ga burinsu na tabbatar da zaman lafiya a nahiyar Afrika dama tsakanin nahiyar da sauran sassan duniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China