Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dakarun Najeriya sun damke mutane hudu dake yiwa Boko Haram cefene
2019-09-04 10:18:42        cri

Mutane hudu dake saya wa mayakan Boko Haram kayayyakin bukatun yau da kullum sun fada komar dakarun sojojin Najeriya a wani wajen binciken ababen hawa, yayin da suke kan hanyarsu ta kaiwa kungiyar 'yan ta'addan kayan masarufi a jahar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar, rundunar sojojin Najeriyar ne ta bayyana hakan a jiya Talata.

Olusegun Adeniyi, kwamandan rundunar sojojin Najeriyar ya bayyana cewa, mayakan sun jima suna amfani da mutanen da ake zargin wajen samar musu da kayayyakin bukatun yau da kullum zuwa sansanonin musamman na mayakan Boko Haram.

Kayayyakin da aka kwace daga hannun mutanen sun hada da man diesel wanda aka boye shi a matsayin man girki, da burodi, da tsabar hatsi, da taburmai, da buhunhuna, da kayayyakin babura, da kuma wasu kayayyakin da mayakan ke amfani da su wajen hada abubuwan fashewa.

Motocin hudu makare da kayayyakin an kone su kurmus a bainar jama'a, bayan da kwamandar sojojin ya ba da umarni, kana ya jaddada aniyar sojojin na gabatar da wadanda ake zargin gaban shara'a.

Jami'in sojojin ya ce, rundunar sojojin tana daukar kwararan matakan karya tattalin arzikin kungiyar Boko Haram ta yadda za ta kasa samun sukunin kaddamar da hare-hare. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China