Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram 33
2019-08-20 19:32:17        cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, sojojin kasar sun yi nasarar kashe a kalla mayakan Boko Haram 33, yayin wani bata kashi a jiya Lahadi.

Wata majiya da ta bukaci a sakaye sunanta ta bayyana cewa, dakarun hadakar kasashen Najeriya, da Chadi ,da Kamaru da Nijar da Benin dake yaki da mayakan Boko Haram a yankin tafkin Chadi, su ma sun shiga bata kashin da aka yi mayakan Boko Haram.

Majiyar ta ce, mayakan Boko Haram da dama sun arce da harbin bindiga a jikinsu, kuma fadan ya yi zafi.

Bayanai na cewa, an shafe kusan sa'o'i uku sassan biyu na musayar wuta, a kan hanyar Gamboru- Dikwa na jihar Borno, yayin da mayakan Boko Haram suka shirya yiwa motocin sojojin kwanton bauna.

Wata majiyar soja ta tabbatar da cewa, sojoji hudu sun ji rauni a musayar wutan.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China