Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tattaunawa bisa sanin ya kamata ce kadai za ta daidaita matsala
2019-09-05 16:06:17        cri

Jagororin shiga tsakani a tattaunawar cinikayya tsakanin Sin da Amurka, sun amince su dauki kwararan matakai na samar yanayin da ya dace don kara yin tattaunawa a watan Oktoba.

An cimma wannan yarjejeniyar ce, yayin wata zantawa ta wayar tarho da mataimakin firaministan kasar Sin Liu He, mamba a hukumar siyasa ta kwamitin koli na JKS kana jagoran kasar Sin a tattaunawar tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka ya yi da wakilin cinikayya na Amurka Robert Lighthizer da sakataren baitul malin Amurka Steven Mnuchin bisa gayyatarsu.

Haka kuma, bangarorin biyu sun amince sun gudanar da zagaye na 13 na tattaunawar tattalin arziki da ciniki na manyan jami'an kasashen biyu a farkon watan Oktoba a birnin Washington, za kuma su rika tuntubar juna kafin ganawar.

A yayin da takaddamar ciniki a tsakanin kasashen 2 take kara tsananta, sassan biyu, sun tsai da kudurin ci gaba da yin tattaunawa, lamarin da ya dace da muradun jama'a da na kasashen duniya. Wannan, wata kyakkyawar alama ce ta daidaita lamarin.

Kasar Sin za ta ci gaba da yin iyakacin kokari da nuna sahihanci wajen yin tattaunawar, sa'an nan za ta ci gaba da tafiyar da harkokinta yadda ya kamata, za ta ci gaba da bin hanyarta yadda ya kamata, za kuma ta kai zuciya nesa wajen daidaita duk wasu batutuwan da ka iya kunno kai (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China