Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi : Kare moriya ba takalar fada ba ne
2019-08-26 19:07:06        cri

Wane ne ya fara tayar da takaddamar cinikayya? Wane ne ya fara kara sanya harajin fito? Kuma wane irin hali na rashin tabbas tattalin arziki duniya ke shirin fuskanta biyo bayan wannan danyen aiki?

Duk mai bibiyan kafofin yada labarai, ya san cewa, Amurka ce ta fara tayar da takaddamar cinikayya, inda a ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2019, ta sanar da sanya harajin farko kan gorar ruwa da karafa dake shiga cikin kasarta daga dukkan kasashen duniya. Daga bisani kuma, Amurka ta sanar da kara sanya haraji kan kayayyakin kasar Sin dake shiga kasarta da darajarsu ta kai dala miliyan uku, inda yanzu maganar da ake har ya kai zuwa dala biliyan 550.

Shin ya dace ita ma kasar Sin ta kare muradunta ko, a'a? Ashe idan har kasar Sin ta mayar da martani, ta yi hakan ne domin ta kare muradunta da na al'ummominta, don haka, kare muradu ba takalar fada ko kara tsananta lamari ba ne.

Amma daga lokaci zuwa lokaci, wasu masana da tsoffin jami'an Amurka gami da 'yan kasar da suka san abin da suke yi, su kan gargadi gwamnatin Amurka mai ci, game da illar matakan da take dauka na kara rura wutar tankiyar cinikayya da kokarin lalata kamfanonin kasar Sin, da ra'ayinta na kashin kai da kokarin yin fatali da duk wasu yarjeniyoyi ko shawarwari da aka cimma da ita. Amma abin ka da wanda ya yi nisa, aka ce baya jin kira. Don haka, " tsuntsun da ya janyo ruwa, shi ruwa zai doka".

Daga lokacin da Amurka ta tayar da takaddamar cinikayya da kasar Sin zuwa wannan lokaci, bangarorin biyu su yi shawarwari kusan zagaye sama da 10, inda wakilan sassan biyu ke cimma matsaya kan yadda za a kawo karshe wannan matsala ba cuta ba cutarwa, amma maganar Amurka a kullum ya kasance ruwan Kwando, da kyar ta ke cika duk wani alkawari da aka yi da ita. Amurka ta fice daga yarjeniyoyin kasa da kasa da dama da aka kulla da ita, inda take fakewa da wani abu ta kuma dora laifi kan sauran kasashe. Ta zama "Gwano, ba ka jin warin jikinka"

Duk da takaddamar cinikayyar dake faruwa tsakanin Sin da Amurka, tattalin arzikin kasar Sin yana samun ci gaba mai inganci, haka kuma yana taka muhimmiyar rawa a tsarin sana'o'in kasa da kasa,bugu da kari, kasuwar kasar Sin tana kan gaba wajen jawo hankalin masu zuba jarin kasashen duniya baki daya. Masu iya magana na cewa, zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana muzuru ko ana shaho sai ya yi.(Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China