2019-08-28 11:27:03 cri |
Babban kantin Costco na Amurka dake da sassa daban-daban a duniya, ya bude reshensa na farko a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin a jiya Talata, inda hanyoyi dake kewaye da shi suka toshe saboda dimbin masu sayayya da ya karba a wannan rana, a karshe dai kantin ya rufe kofarsa da wuri don tabbatar da tsaron jama'a. A hannu guda kuma, a wannan rana muhimman ma'auni uku na kasuwar hannun jarin Amurka sun rika samun raguwa, amma kuma farashin hannun jari na kamfanin Costco ya karu da kashi 5 cikin dari.
Wannan kamfani na kasar Amurka ya samu karbuwa kwarai da gaske a kasar Sin, kana kuma hannun jarinsa yake tafiya a kasuwar hannun jari ta Amurka, abun da ya zama shaidar dake nuna yin biris da umarnin da shugaban Amurka Donald Trump ya bayar a kwanakin baya, wanda ya nemi kamfanonin kasar su janye jikinsu daga kasuwar kasar Sin. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China