Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba wanda zai katse huldar tattalin arzikin Sin da Amurka
2019-08-30 10:43:00        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng ya yi tsokaci game da umurnin da wasu jami'an Amurka suka bayar, na janye kamfanonin kasar daga kasar Sin da kuma neman fitar da manufa ta daban na yin ciniki da kasar Sin, inda ya ce a ganinsa, muradun Sin da Amurka na bai daya ne dake harhaduwa da juna sosai, don haka babu wanda zai katse wannan hulda ko kadan.

Gao Feng ya bayyana haka ne a gun taron manema labarai da aka yi jiya, inda ya kara da cewa, katse huldar tattalin arzikin kasashen biyu zai haifar da babbar illa, kuma wanda ya aiwatar da shi ya kan ci mai shi, wato ba lahanta moriyar kamfanoni da jama'ar Amurka kadai zai yi ba, har ma da kawo barazana ga sana'ar samar da kayayyaki a duniya, da lalata ciniki da tattalin arzikin duniya. Ya ce, asalin huldar ciniki da tattalin arzikin Sin da Amurka shi ne hadin kai da cin moriya tare, kamata ya yi su kasance abokan juna a maimakon yin gaba da juna. Sin na maraba da kamfanonin kasa da kasa ciki hadda Amurka, da su zuba jari da kuma tafiyar da harkokinsu a kasar Sin, Sin kuma za ta ci gaba da shimfida yanayi mai nagarta ta fuskar kasuwanci. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China