Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda Amurka ta kutsa kai cikin yankin tekun Nansha ya lalata zaman lafiyar yankin tekun kudancin kasar
2019-08-29 14:20:48        cri

Yau Alhamis Babban Kanal Li Huamin, kakakin dakarun kasar Sin da aka jibge a yankin kudancin kasar ya bayyana cewa, a ranar 28 ga wata, jirgin ruwan yaki kirar Wayne E. Meyer na sojojin ruwan Amurka ya kutsa kai cikin yankin tekun da ke kusa da duwatsun tsibirin Nasha na kasar Sin ba tare da samun izni daga gwamnatin kasar Sin ba.

Mayakan saman kasar Sin da aka jibge a yankin kudancin kasar sun bi sawun jirgin don sanya masa ido, da sanin inda ya fito, kana suka yi masa gargadi bisa doka don korarsa daga yankin tekun baki daya. Don haka kasar Sin ta bukaci Amurka da ta daina harzuka kasar Sin ta hanyar shiga yankunan ruwanta ba tare da izni ba don magance abkuwar hakan nan gaba.

Kalaman Amurka na cewa, wai samun 'yancin zirga-zirga da wucewa ta yankin ruwan, tamkar fatali ne da dokokin kasa da kasa da mulkin danniya ta fuskar zirga-zirga. Lamarin da ya keta 'yancin kasar Sin da ma muradunta a fannin tsaro, kana ya lalata zaman lafiya da kwanciyar hankali da ake samu a yankin tekun kudancin kasar.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China