Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin ma'aikatar cinikin Sin ya yi jawabi game da matakin Amurka na kara sanya haraji kan wasu kayayyakin da take shigo da su daga kasar Sin
2019-08-24 21:14:31        cri
Kakakin ma'aikatar cinikin kasar Sin ya yi jawabi game da matakin Amurka na kara sanya haraji kan wasu kayayyakin da take shigo da su daga kasar Sin.

A yau ne, kasar Amurka ta sanar da kara sanya haraji kan wasu kayayyakin da take shigo da su daga kasar Sin da darajarsu ta kai dala biliyan 550, Sin ta ki amincewa da matakin. Wannan mataki bisa ra'ayin bada kariya ga cinikayya da yin matsin lamba ga Sin ya saba wa ka'idojin girmama juna, da samun moriyar juna cikin adalci, ya kuma kawo illa ga tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban da odar ciniki ta kasa da kasa, kuma a cewar kakakin, wanda ya shuka zamba, shi zai yi girbinsa. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China