Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin Amurka na nuna shaawa kan kasuwannin Sin duk da takaddamar ciniki
2019-09-03 13:33:25        cri

Yayin da takaddamar tattalin arziki da ciniki a tsakanin kasashen Amurka da Sin ke kara yin kamari sakamakon matakan Amurka, kasar da har ta ingiza kamfanoninta da su janye daga kasar ta Sin, kamfanonin Amurka da dama suna neman inganta hulda a tsakaninsu da kasar Sin. Gidan telibijin na CNBC na Amurka ya labarta a ranar 1 ga wata cewa, kamfanonin Amurka kalilan ne suke shirya janyewa baki daya daga kasar Sin, saboda yin hakan zai iya lalata fifikonsu na yin takara sosai.

A kwanan baya, babban kamfanin sarrafa kayayyakin gorar ruwa na Novelis, mai hedkwata a Atlanta na Amurka ya sanar da shirinsa na habaka ciniki a kasar Sin. Kamfanin ya yi hasashen cewa, kasar Sin za ta samu kyakkyawar makoma a matsayinta na kasuwar kera da sayar da motoci mafi girma a duniya, kana yana da kyakkyawar dama saboda kasar Sin ta karkata ga sana'ar kera motoci masu amfani da sabbin makamashi.

Shi ma Craig Allen, shugaban kwamitin kula da ciniki tsakanin Amurka da Sin ya nuna cewa, yawancin kamfanonin Amurka da ke yin ciniki a Sin sun fahimci cewa, nan gaba kasar Sin za ta kasancewa daya daga cikin jigon ci gaban tattalin arzikin duniya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China