Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnan jihar Bornon Nijeriya ya bukaci a sake bitar tsarin tsaron kasar
2019-08-24 15:28:51        cri
Gwamnan Jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin Nijeriya, Babagana Zulum, ya jaddada bukatar sake bitar tsarin tsaron kasar da nufin kara masa karfi da inganci.

Gwamnan ya bayyana haka ne jiya, yayin da yake yi wa shugaban Kasar Muhammadu Buhari, bayani game da hare-haren BH na baya-bayan nan a kauyukan jihar, inda ya shaidawa manema labarai cewa, akwai bukatar jami'an tsaro su rubanya kokarinsu na kawo karshen rikicin BH.

Babagana Zulum ya ce 'yan tada kayar bayan sun shiga yankunan ne ba tare da sun fuskanci kalubale ba, domin an yi ammana jami'an tsaro da 'yan sintiri na CJTF, sun tsere cikin dazuka domin buya.

Ya kara da cewa, za a karfafa 'yan sintirin domin inganta ayyukansu, la'akari da muhimmancinsu ga aikin kawo karshen ta'addanci a jihar.

Bugu da kari, Gwamnan ya alakanta karuwar ayyukan BH da ta'azzara kalubalen tsaro a jihar, da kasancewarta mai iyaka da kasashen 3 da suka hada da Nijar da Chadi da Kamaru, wato iyakokinta a bude suke, lamarin dake bada saukin shiga. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China