Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsoffin mayakan Boko Haram a yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru sun ajiye makamansu
2019-07-05 10:04:25        cri
Shugaban kwamitin kwance damarar makamai da sake tsugunar da tsoffin 'yan tawaye na kasar Kamaru (NCDDR) Francis Fai Yengo ya bayyana a jiya Alhamis cewa, cibiyarsa za ta tsugunar da tsoffin mayakan Boko Haram 150 wadanda suka ajiye makamansu bisa radin kansu.

Francis Fai Yengo ya shaidawa manema labarai cewa, tsoffin mayakan da suka ajiye makaman nasu, za su ci gajiyar wani shiri na samun horo a fannonin aikin gona da kiwon dabbobi da kasuwanci da sana'o'in hannu yayin da suke zaune a cibiyar.

Kasar Kamaru dai tana fuskantar kalubalen tsaro ne a yankuna biyu na kasar dake magana da Turanci Ingilishi, wato arewa maso yammaci da kudu masu yammaci, inda 'yan aware ke neman ballewa, da kuma 'yankin arewa mai nisa na kasar, inda 'yan tawayen Boko Haram ke zafafa kai hare-hare kan dakarun gwamnati da kuma fararen hula.

A shekarar da ta gabata ce shugaba Paul Biya na Kamaru, ya kafa kwamitin na NCDDR, a wani mataki na kaucewa amfani da tsauraran matakai, da sanya ido kan yadda za a kwance damarar makamai da sake tsugunar da tsoffin mayakan Boko Haram da 'yan aware dake yankunan kasar dake magana da Turancin Ingilishi.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China