Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamaru ta samar da taimako ga kungiyoyin 'yan sintiri domin yaki da Boko Haram
2019-08-18 15:48:41        cri

Gwamnatin Kamaru ta samar da kayayyakin aiki da taimakon kudi ga jami'an sintiri dake unguwanni, wadanda ake kira da 'yan sintiri ko 'yan banga, a yankin arewa mai nisa dake kasar.

Gwamnan yankin, Midjiyawa Bakary, ya shaidawa manema labarai yayin wani bikin mika taimakon a yankunann Logone da Shari cewa, wannan lokacin ne da yara za su koma makaranta kuma galibin 'yan sintiri za su matse kaimi kan ayyukansu dake mayar da hankali ga kare fararen hula da yankunan kasa. Ya ce saboda haka ne shugaban kasar ya yanke shawarar taimaka musu da kayayyakin aiki da kudi.

Gwamnan ya kara da cewa, kungiyoyin 'yan sintiri sun taimaka sosai a yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram, kuma wannan taimakon da aka ba su, zai taimaka gaya wajen karfafa musu gwiwar inganta ayyukansu.

Kayayyakin sun hada da Babura da tocilan da wayoyin sadarwa da na'urar gano makami da rigunan ruwa da kwale-kwale da kuma kudi.

A cewar rundunar sojin Kamaru, tun daga shekarar 2014, 'yan sintiri da adadinsu ya kai 14,000 a yankin, suke taimaka mata da bayanan sirri, inda har a wani lokacin suke fito na fito da masu rajin jihadi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China