Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan wadanda suka rasu sanadiyar harin Boko Haram ya karu zuwa mutum 70
2019-07-29 19:36:27        cri
Rahotanni daga jihar Borno ta arewa maso gabashin Najeriya na cewa, yawan wadanda suka rasa rayukan su, sakamakon harin karshen mako da ake zargin kungiyar Boko Haram da kaddamarwa, ya karu zuwa mutane 70.

Tsakanin jiya Lahadi da yau Litinin, ma'aikatan ayyukan jin kai, sun gano karin gawawwakin mutane da aka hallaka a karamar hukumar Nganzai, inda harin ranar Asabar ya rutsa da al'ummun kauyuka 3.

Wata majiya ta tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, a kalla gawawwakin mutane 15 aka gano da yammacin jiya Lahadi. Mafi yawancin su kuma an gano su ne a wasu dazuka, dauke da raunukan bindiga.

Abbagana Ali, jagoran kungiyar tsaro ta 'yan sa kai ko Civilian JTF ne a yankin, ya kuma bayyana cewa, mayakan Boko Haram sun hallaka kauyawa da dama a ranar Lahadi, lokacin da suke gudanar da jana'iza a wata makabarta. Maharan sun yiwa kauyen dirar mikiya ne cikin wasu motocin da aka daurawa manyan bindigogi dake iya kakkabo jiragen sama, suka kuma bude wuta kan mai uwa da wabi.

Shugaban karamar hukumar Nganzai Muhammad Bulama, ya bayyanawa majiyar mu cewa, ana hasashen mayakan Boko Haram din sun kaddamar da harin ne, a matsayin ramuwar gayya na wasu dakarun su da aka hallaka a yankin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China