Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Najeriya ya tura tawaga ta musamman zuwa Afirka ta Kudu dangane da harin da ake kaiwa 'yan Najeriya a kasar
2019-09-04 09:09:00        cri

A jiya Talata ne, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya nada manzo na musamman zuwa kasar Afirka ta Kudu, sakamakon rahotannin harin da ake kaiwa 'yan Najeriya dake zaune a kasar.

Wata sanarwar da fadar shugaban Najeriyar ta fitar ta bayyana cewa, shugaba Buhari ya kuma umarci ministan harkokin wajen Najeriya, da ya gayyaci babban kwamishinan kasar Afirka ta Kudu dake kasar, don ya yi masa bayani kan halin da ake ciki tun ranar 29 ga watan Agustan wannan shekara.

A ranar Alhamis ne ake sa ran manzon musamman da shugaban Najeriya ya tura, zai isa birnin Pretoria, inda zai bayyana wa shugaban Afirka ta Kudu rashin jin dadin shugaba Buhari, ya kuma tattauna da shi kan wannan yanayi.

An dai shirya shugabannin kasashen biyu, za su gana ne a watan Oktoba, inda za su tattauna batutuwan da suka shafi kasashensu da ma 'yan Najeriya dake kasar Afirka ta Kudu.

A ranar Litinin ne, aka kaddamar da sabbin hare-hare a birnin Johannesburg, inda aka ba da rahoton cewa, hare-haren sun rutsa da wasu 'yan Najeriya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China