Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Argentina ta doke Najeriya a gasar kwallon Kwando ta hukumar FIBA
2019-09-02 20:02:33        cri
Argentina ta doke Najeriya da maki 94 da 81, a gasar kwallon Kwando ta duniya da hukumar FIBA ta shirya, wadda yanzu haka ke ci gaba da gudana a nan kasar Sin. Argentina ta samu nasara kan kungiyar Najeriya ne a wasan ta na biyu na rukuni a yau Litinin.

Dan wasan Argentina Luis Scola, shi ne wanda ke kan gaba da yawan maki a wasan, inda ya samu maki 23, yayin da kuma Facundo Campazzo ya kara yawan makin sa zuwa 14. A bangaren 'yan wasan Najeriya kuwa, Josh Okogie ne ke kan gaba da maki 18, ya kuma taimaka wajen zura kwallaye 5 a raga.

Kafin hakan, Najeriya ta sha kashi hannun kungiyar kasar Rasha da maki 82 da 77, a wasan ranar Asabar din da ta gabata. Kungiyar Najeriyar ta yi fatan samun nasara kan Argentina da wata kasar ta daban, kafin kaiwa ga wasan kungiyoyi 16 a zagaye na 2 na gasar. Yayin da ita ma Argentina ke burin sake lashe wani wasan a gaba, da samun karin tazarar maki domin kaiwa ga wasan kungiyoyi 16. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China